Daga Muhammad Kwairi Waziri
A safiyar yau Laraba ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kauyukan Yadagungume da Limi da ke karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi inda suka kashe mutum uku yayin da wani mutum guda ya samu raunuka, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Wakilinmu ya samu labarin cewa wadanda aka kashen sun hada da Shuaibu Salihu (17) da Ruwa Ali wanda aka fi sani da Mai Inji (45) da Sunusi Isah Burra.

Wata majiya a garin Ningi da ba ta so a ambaci sunan ta ta shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12 na safiyar Laraba.
Ya ce ‘yan bindigar sun fara kai farmakin ne a unguwar Yadagungume inda suka fara harbe-harbe ba da dadewa ba, lamarin da ya sa mutanen kauyen da tuni suka yi barci suka firgita kafin daga bisani su kai farmaki kauyen Limi, duk a gundumar Burra ta karamar hukumar.
Majiyar ta ce, “Daga bayanin da na samu, ‘yan bindigar da har yanzu ba a san adadinsu ba sun fara kai wa Yadagungume hari da harbin bindiga, sai wani yaro ya fito ya yi ihu, sai suka harbe shi.
“Yan bindigar sun yi awon gaba da mutane biyu, kuma ko ta yaya daya daga cikinsu ya tsere. Amma ba mu san abin da ya faru ba, daga baya suka harbe wani da suka tafi tare. Wasu mata ne da suka je gona da sanyin safiyar yau suka ga gawarsa suka tada kararrawa.