fbpx
Friday, August 12
Shadow

Yan bindiga sun kai hari Millennium City a jihar Kaduna sunyi garkuwa da mutane bayan da suka ce zasuyi garkuwa da gwamnan jihar

‘Yan bindiga sun kai hari Mullinnium City dake karamar hukumar Chikum a jihar Kaduna inda sukayi gakuwa da mutane da dama.

‘Yan bindigar sun kai harin ne a daren ranar litinin kuma sun dauki tsawo wasu ‘yan awanni suna gudanar da ta’addancin nasu.

Makonni uku da suka gabata ma ‘yan bindigar sun kai hari Mullinnium City din inda har suka kashe wani babban jami’in JTF tare wani mazaunin yankin.

‘Yan bindigar sun kai wannan harin ne bayan da suka bayyana cewa zasuyi garkuwa da gwamnan jihar Kaduna wato Nasiru Ahmad El Rufa’i da kuma shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Leave a Reply

Your email address will not be published.