Wasu yan bindiga sun kashe mutane bakwai a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
Harin na baya-bayan nan ya zo ne sa’o’i 24 bayan ‘yan bindiga sun kashe mutane 48 a kauyuka uku da ke karamar hukumar Bakura ta jihar.
A cewar wata majiya mai tushe a kauyuka biyu na Maradun, Faru da Kauyen Minane, an kai harin ne da yammacin ranar Asabar, 7 ga watan Mayu.