‘Yan Bindiga sun kai munanan hare-hare kauyukan jihar Taraba inda suka rika yiwa matan aure da ‘yan mata fyade.
Lamarin ya farune a kananan hukumomin Gassol da Karim Lamido.
‘Yan Bindigar sun shiga kauyen Kambari dake karamar hukumar Karim Lamido, kauyen bai da hanya me kyau da mota zata iya shiga.
Dan haka ‘yaj Bindigar sun ci karensu ba babbaka, sun kori jami’an tsaron ‘yansanda da Vigilante dake garin inda suka shiga suka rikawa matan aure da ‘yan mata fyade.
‘Yan garin babu yanda suka iya haka suka rungumi kaddara saboda babu wasu jami’an tsaron da suka kai musu dauki.
Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen kauyukan Gwammo, Wurno, Tungan Kaya, Gidan Kawoyel, da Ali Kwala duk sun tsere saboda ayyukan ‘yan Bindigar.
Duka wadannan kauyukan na karamar hukumar Karim Lamido ne dake jihar ta Taraba.
Rahoto yace ‘yan Bindigar na jawo dare da rana dauke da makamansu a yankunan ba tare da wata matsala ba.
‘Yan Bindigar sun zama maau hukunci a kauyukan inda suke sace matan aure da sauran mutane ba tare da wata matsala ba.
Hakanan ‘yan Bindigar sun dauki kananan yara suna musu aikin bada bayanan sirri.
Da aka tuntubi kakakin ‘yansandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi ya gayawa Daily Trust cewa, basu samu Rahoton faruwar hare-haren ba.