fbpx
Sunday, August 7
Shadow

‘Yan bindiga sun kaiwa hukumar zabe ta INEC hari a jihar Enugu

‘Yan Bindiga sun kaiwa hukuma gudanar da zabe ta INEC hari a Igboeze dake arewan jihar Enugu, sun jiwa mutane biyu rauni.

Kwamshinan hukumar dake magana da yawunta, Fetus Okoye ne ya bayyana hakan a yau ranar alhamis inda yace an kai masu harin ne yayin da suke cigaba da yiwa mutane rigistar katin zabe.

Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun lalata mashina biyu da hukumar ke aiki dasu sannan kuma mutane biyu da suka samu raunika an kwantar dasu a asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published.