fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

‘Yan Bindiga Sun Kara Kashe Mutum Uku Sun Jikkata 6 A Katsina

Bayan kashe sama da mutum goma sha biyar a kauyen Unguwar Gizo da ke karamar hukumar Faskari, a daren jiya jumaa sun kai hare haren a garin Matseri da ke gundumar Sheme da ke karamar hukumar Faskari, inda suka kashe mutum ukku har lahira sun Kuma harbi mutum shidda, wanda yanzu haka suna kwance a asibiti.

 

 

Wani mazaunin garin ya shaidawa RARIYA ta waya cewa “yan bindigar sun zo ne, kan mashina dauke da bindigogi, sun shigo garin Matseri, inda suka kashe mutum ukku, suka harbi mutum shidda, sun samu raunuka daban-daban.

Karanta wannan  'Yan ta'addan ISWAP sun kai sabon hari a Maiduguri sun kashe dan samda guda

 

Rohatannin da RARIYA ke samu duk a daren jiya Juma’a Yan bindigar sun shiga kauyukan Yar Nasarawa da Unguwar Alhaji Babba da Kuma Unguwar Kanya duk sun kwashe masu dabbobi a daren jiya.

 

 

Daga shekaran jiya zuwa yau, an kashe mutum sama da Sha tara a kauyukan Unguwar Gizo da Matseri duk karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.