fbpx
Friday, July 1
Shadow

Yan bindiga sun kashe akalla mutane 19 a kauyukan Benuwe

‘Yan bindigar, a garin Tiortyu na karamar hukumar Mbakor Tarka, sun kashe mutane 10.

Hakan yasa wasu fusatattun matasa da safiyar Talata sun tare babbar hanyar gwamnatin tarayya da ta tashi daga Makurdi babban birnin jihar zuwa Gboko domin nuna rashin amincewa da lamarin.

Toshewar ta haifar da cinkoso saboda motsin ababen hawa ya tsaya cak na sama da awanni 10.

Tyortyu birni ne na tauraron dan adam (satellite village) a kan babbar hanyar Makurdi- Gboko a cikin karamar hukumar Tarka a jihar Benue.

Wani dan unguwar da ya tsallake rijiya da baya mai suna Tersoo Utume, ya shaida wa jaridar The Nation cewa ‘yan bindigar sun far wa al’ummar da ke barci da misalin karfe biyu na safiyar ranar Talata inda suka rika bi gida-gida suna harbin mutanen kauyen.

Karanta wannan  Sai mun biya ‘yan bindiga N400m a matsayin kudin haraji kafin su bari mu girbi amfanin gonakinmu – Shugaban al’ummar Kaduna

A kauyen Tse-Sumaka, wasu ‘yan bindiga sun kashe manoma tara a kusa da reshen Umenger da ke gundumar Mbadwem a karamar hukumar Guma a ranar Litinin.

Babban mataimaki na musamman ga Gwamna Samuel Ortom kan harkokin yada labarai James Igbudu, wanda ya tabbatar da kisan, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kare al’ummarsa daga wadanda ake zargin makiyaya ne.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Benue, Kate Aenee, SP, ta ce tana kan hanyarta ta zuwa wurin da lamarin ya faru tare da kwamishinan ‘yan sandan kuma za ta fitar da sanarwa nan ba da jimawa ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.