fbpx
Monday, August 15
Shadow

‘Yan bindiga sun kashe dalibar jami’ar LAUTECH tare da mai Otal bayan sun karbi kudin fansa

‘Yan bindiga sun kashe dalibar jami’ar LAUTECH ta jihar Osun tare da wani mai Otal bayan sunyi garkuwa dasu a kwanakin baya.

Dalibar ta kasance a shekarar karshe a jami’ar kuma yajin aikin da kungiyar malamai ta ASUU keyi ne yasa ta nemi aiki a Otal din.

Wanda ‘yan bindigar sukayi garkuwa da ita suka kasheta tare da mai gidan nata, inda wasu rahotanni suka bayyana cewa har naira miliyan biyar suka bayar kudin fansa amma duk da haka sai da suka hallaka su.

Karanta wannan  Zamu fara baiwa talakawa miliyan 40 tallafin naira dubu biyar a kowane wata, cewar gwamnatin tarayya

Hukumar ‘yan sanda batayi tsokaci akan wannan lamarin ba amma jami’ar da dalibar take ta tabbatar da faruwar lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.