fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

‘Yan bindiga sun kashe dan sanda sunyi garkuwa da dan kasar Sin a jihar Kwara

‘Yan bindiga sunyi garkuwa da wani dan kasar sin kuma sun kashe jami’in dan sanda a harin da suka kai karamar hukumar Moro a jihar Kwara.

‘Yan bindigar sun babbaka motar hukumar kafin daga bisani suka tsere, kuma sun jigata wani jami’in wanda yanzu yake jinya a asbiti.

Mai magana da yawun hukumar na jihar, Okasanmi Ajayi ne ya tabbatarwa manema labarai wannan labarin inda yace zasu tabbatar da cewa sun ceto dan kasar sin din.

Kuma ya kara da cewa basu ji dadin kashe masu jami’i da aka yi ba sannan zasu kama wa’yanda suka aikata wannan laifin don a hukunt su.

Leave a Reply

Your email address will not be published.