Yan bindiga dauke da makamai sun yi garkuwa da mutane goma sha hudu a jihar Neja tare da kashe wani dan sanda da jikkata wani a karamar hukumar Mariga da ke jihar ta Neja.
Wannan Lamarin dai ya faru ne a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba 2020.
Vanguard ta aminta da cewa an garzaya da dan sandan da ya samu rauni zuwa babban asibitin Minna.
Hakanan awanni 12 baya Lamarin an sake sace wasu mutane 7 a kauyen Shamuyambu dake yankin Kusherki na karamar hukumar Rafi.