Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Tungar Ruwa da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfara, inda suka kashe mutane da dama a harin.
Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa, da sanyin safiyar Laraba ne ‘yan bindigar suka far wa kauyen, inda suka yi ta bincike daukacin kauyen tare da harbin mutanen kauyen.
Ya kara da cewa an kashe mutanen kauyen guda tara, ciki har da hakimin kauyen da aka yanka a gaban mutanensa.
Majiyar ta ce, “Sun kai farmaki gidan hakimin kauyen, suka kawo shi ga jama’a, suka yanka shi har ya mutu.”
Ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da dabbobi tare da yin awon gaba da kayan shaguna da dama tare da kwashe kayan abinci na miliyoyin naira.
Ya ce tuni mazauna unguwar musamman mata da yara suka tsere daga kauyen saboda fargabar sake kai wani hari.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO), SP Mohammed Shehu, bai samu damar yin tsokaci ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto.