fbpx
Monday, August 15
Shadow

‘Yan bindiga sun kashe insfetoci biyu tare da wani dan Indiya a wani kamfani dake jihar Imo

‘Yan bindiga sun kai hari wani kamfani dake kera tukwanen bandaki na ceramic a jihar Imo ranar juma’a da misalin karfe takwas na dare.

Inda hukumar ‘yan sanda suka bayyana cewa ‘yan bindigar sun kashe infetocin ‘yan sanda guda biyu tare da direbobin kamfanin guda biyu.

Yayin da kuma suka hada da wani dan Indiya suka kashe shi duk dai a harin da suka kaiwa kamfanin dake Ajaokuta a Owerre.

Hukumar ‘yan sandan ta bayyana cewa insfetocin sun rasa rayukansu ne yayin da suke musayar wuta da ‘yan ta’addan a harin da suka kaiwa kamfanin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.