fbpx
Monday, August 15
Shadow

‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro guda bakwai a jihar Imo

‘Yan bindiga sun kai hari Orogwe dake kudancin Owerri inda suka kashe jami’an tsaro guda bakwai a yankin.

Wannan lamarin ya faru ne a daren ranar litinin, inda aka samu labari cewa a motoci biyu da babur guda suka kai wannan harin.

Kuma akwai mutanen dake jinya a asibiti bayan sun jigatasu a harin da suka kai, duka jami’an da suka kashe masu gadi ne.

Kuma mai magana da yawun hukumar jihar, Michael Abattam ya tabbatar da faruwar wannan lamarin inda yace sun fara gudanar da bincike don gano mutanen da suka kai harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.