fbpx
Friday, August 12
Shadow

‘Yan bindiga sun kashe mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina

‘Yan bindiga sun kashe kwamishinan hukumar ‘yan sanda na yankin Dutsinma a jihar Katsina, ACP Aminu Umar tare wani jami’i guda a karamar hukumar Safana.

‘Yan bindigar sun kashe sune a wani harin kwantan bauna da suka kaiwa hukumar.

Mai magana da yawun hukumar na jihar Katsina, Gambo Isa ya tabbatar da wannan rahoton inda yace ‘yan bindigar su kusan 300 suka zo akan babura.

Kuma sunyi nasarar kashe masu jami’an ne yayin da suke musayar wuta a daren jiya da misalin karfe 11:30 na dare.

Leave a Reply

Your email address will not be published.