Innalillahi wa inna ilaihi raji’un
A jiya, Larabane ‘yan bindiga a tsakanin hanyar Zamfara zuwa Katsina suka kashe Dr. Muhammad Bello Hassan na jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.
‘Yan Bindigar sun kashe malaminne a a hanyarshi ta dawowa daga Zamfara a wani aiki da yaje yi.
Kamin rasuwarsa yana koyarwane a tsangayar Tattalin arzikin Noma dake jami’ar.
An yi jana’izar sa kamar yanda addinin Musulunci ya tanada.
Muna fatan Allah ya jikanshi da rahama.