‘Yan bindiga sun kashe mutane 11 a garin Ghadi dallke karamar hukumar Rabah a jihara Sokoto.
Wannan lamarin ya faru ne ranar asabar kamar yadda mazaunin yankin ya bayyana, inda yace sun kai harin ne da misalin karfe 12 na yamma.
Sakataren hakimin garin Ghadin, Tukur Muhammad yace maharan sunje gonakin garin sun kashe manona babu dalili.
Kuma sun so yin garkuwa da wasu mutane amma ‘yan banga sunyi hanasu tafiya da kowa.