fbpx
Thursday, August 18
Shadow

‘Yan Bindiga sun kashe manoma 7 da sace Mutane 30 a Katsina

Akalla Manoma 7, ciki hadda wata mata me sabon jariri aka kashe a kauyukan Unguwar Maigayya, Tashar Bama, da Dogun Mu’azu duk dake karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina.

 

Ibrahim Danjuma Machika, dan majalisa me wakiltar yankinne a majalisar jikar katsina ya bayyana haka a zaman majalisa na Ranar Litinin inda yace lamarin ya farune a karshen makon da ya gabata.

Ya bayyana cewa harin ya faru ne da rana tsaka inda kuma aka sace mutane 30. Ya bayyana cewa mutanen yankinsa na fama da fargaba.

 

“Our people now live in full fear as the terrorists now carry out attacks in our villages in broad daylight. They killed the people, carted away their properties and abducted as many people as they could,” he said

Karanta wannan  'Yan ta'addan ISWAP sun dauke manoma shida a jihar Borno

 

Shima dan Majalisa me wakiltar Safana, Abduljalal Haruna Runka dana Dutsinma,  Mohammed Khamis duk sun bayyana cewa yankunansu na fama da hare-hare. Kakakin majalisar, Tasiu Zango yayi Allah wadai da lamarin hare-haren inda yace a mikawa gwamnan jihar, Aminu Bello Masari Bukatar habaka Tsaro a yankin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.