fbpx
Monday, August 15
Shadow

‘Yan bindiga sun kashe mutane 11 a sabon harin da suka kai jihar Zamfar

‘Yan bindiga sun kashe mutane 11 a sabon harin da suka kai karamar hukuma Maru dake jihar Zamfara.

Sun kai harin ne da safitar ranar lahadi a yanukanan Kango da kuma Dangulbi dake karamar hukumar ta Maru.

Kuma yawancin mutanen da suka kashe manoma ne da suka je girbe abinda suka shuka, yayin da kuma wasu mazaunna yankin suka ce mutane 18 ne ‘yan bindigar suka kashe.

Amma mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda na jihar Muhammad Shehu ya bayyana cewa mutane 11 kuma hukuma ta kai masu gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.