fbpx
Friday, February 26
Shadow

Yan Bindiga sun kashe mutane 19 a sabon harin da suka kai Kaduna

Wasu ƴan bindiga sun kai hari Tashar Kaɗanya a yankin Kutemeshi na ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna inda suka kashe mutum 19 a ranar Asabar.

Mazauna yankin sun ce ƴan bindigar sun shigo ne misalin ƙarfe 5 na yamma inda suka buɗe wuta suka abka shagunan mutane suka kwashi kayayyaki da suka haɗa da wayoyin salula.

Bayan kashe mutum 19, sun kuma raunata mutum 10, kamar yadda wani mazauni yankin ya shaida wa BBC.

Ya ce da safiyar Lahadi aka yi wa mamatan jana’iza.

Ƴan bindiga masu fashi da satar mutane sun addabi yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna inda suka tarwatsa ƙauyuka tare da tilastawa dubbai gudun hijira.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *