‘Yan Bondi sun kai hari a kauyen Adei, Kutura, Tantatu dake karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Sun kashe mutane 2 da kuma kona gine-gine.
Hukumar ‘yansandan jihar bata tabbatar da harin ba amma tsohon shugaban karamar hukumar ya tabbatarwa da Channels TV harin.
Gidan TVn yace akalla gidaje 30 ne aka kona da kuma wata coci daya.