Lamarin ya farune a kauyen gurbin Magarya dake karamar hukumar Jibia inda ‘yan Bindigar suka kashe mutane 3 suka jikkata wasu 3.
Wani mazaunin garin, Halliru Haladu ya bayyanawa Premium times cewa ‘yan Bindigar sun kai harinne da misalin karfe 10 na dare kuma sun je ne akan mashina.
Ya kara da cewa badan sojoji da ‘yan Bijilante ba da ‘yan Bindigar sun gama da kauyen nasu amma kamin sojojin su kai dauki tuni har an kashe mutane 3.