fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

‘Yan bindiga sun kashe mutane bakwai da suka je biki a jihar Imo

‘Yan bindiga sun kashe mutane guda bakwai ranar lahadi bayan sunje gidan biki a jihar Imo.

‘Yan bindigar sun bude masu wuta ne yayin da suke hanyarsu ta komawa gida dake Otolu a karamar hukumar Oru a gabashin jihar Imo.

Shugaban Otolu Nnamdi ne ya bayyanawa mutane hakan inda yace sun bude masu kuma sun kashe bakwai a cikinsu, kuma biyar sun bace yayin da biyu suka samu rauni.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Rundumar sojin sama sun hallaka shugaban 'yan ta'addan Boko Haram da tawagarsa a jihar Maiduguri

Leave a Reply

Your email address will not be published.