fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Yan bindiga sun kashe mutane biyu, sunyi garkuwa da mutane uku a Ayobo dake jihar Legas

Yan bindiga sun kai hari anguwar Ayobo dake jihar Legas tsakanin ranar juma’a zuwa lahadi inda suka mamaye wasu gudaje suka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da mutane uku.

Sakataren masu gidajen anguwar Mr. James ya bayyanawa manema labarai na NAN cewa yan bindigar da sukayi kashe mazaje biyu kuM sukayi garkuwa da mata biyu ran juma’a sun sake yin garkuwa da wani a ranar lahadi.

Kuma ya kara da cewa yan bindigar sun tafi dasu ne cikij jejin dake bodar Legas da Ogun a cikin jirgin kwale-kwale.

Leave a Reply

Your email address will not be published.