Hallau yan bindiga sun kara kai hri jihar Imo a karamar hukumar Orlu ind suka budewa jama’a wuta har saida jami’an tsaro suka iso wajen.
Wanda hakan yayi sanadiyar rayukan al’umma da dama kuma suka kona masu gidajensu. Amma mai magana da yawun yan sanda na jihar, mike Abattam bai rigada ya tabbatar da faruwar lamarin ba.
Jihar Imo na daya daga cikin jihohin da yan bindiga suka takurawa yayin da a makon daya gabata aka dakatar da rigistar katin zabe a jihar, bayan yan bindigar sun kashe ma’aikacin hukumar INEC dake gudanar da zabe ta kasa.