Mutane da dama sun rasa rayukansu bayan da ‘yan bindiga suka kai hari yankin Igama a karamar hukumar Okpokwu a jihar Benue.
Kuma ‘yan bindigar sun kona gidaje da dama a mummunan harin da suka kai ranar ladadi.
Mai magana da yawun ‘yan sanda ta jihar, Catherine Anene ta tabbatar da faruwar wannan kamarin inda tace an saka jami’ai sosai a yankin amma har yanzu ba a tabbatar da dadin mutanen da harin ya shafa ba.