‘Yan bindiga sun kashe mutane hudu sunyi garkuwa da mutane 15 a sabon harin da suka kai jihar Kaduna.
Sun kai harin ne a kauyen Uburu dake Kufena a karamar hukumar Kagoro ranar litinin din data gabata.
Inda aka samu labari cewa sun kai harin ne daddare ranar ta litinin din inda suka kashe mutane uku a cikin kauyen sukayi garkuwa da mutane 15.
Yayin da kuma suka kashe na hudu yayin dayake dawowa daga wurin aikinsa.