Gwamnatin jihar Kaduna ta fada a ranar Lahadi cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane bakwai a Jihar.
Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Mista Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Lahadi a Kaduna.
Aruwan ya ce, “a wani abin bakin ciki, hukumomin tsaro sun ba da rahoton cewa ‘yan bindigar sun kai hari kan wasu mutane a kauyen Kajinjiri, karamar hukumar Igabi, kuma sun kashe mazauna 2″.
Ya ce mutum daya ya samu rauni a harbin bindiga kuma yana karbar magani a wata cibiyar lafiya da ke kusa.
Hakazalika, a kauyen Rago, kuma a karamar hukumar Igabi, ‘yan bindiga sun kashe wasu mazauna yankin 2,”.
Ya kuma bayyana cewa a wani lamarin na daban, ‘yan bindiga sun mamaye tashar Kutura, cikin karamar hukumar Kajuru, inda suka kashe mazauna wurin 3.
Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir El-Rufai yayi Allah wadai da wadannan hare-haren, ya kuma jajantawa dangin wadanda aka kashe a duka hare-haren biyu, tare da yin addu’o’in neman jikan rayukansu.