fbpx
Saturday, December 3
Shadow

‘Yan Bindiga Sun Kashe Shi Bayan Sun Karbi Kudin Fansarsa Naira Milyan Shida

HAKA ZA A CI GABA DA KASHE MU BABU ABUN DA ZA A YI?

‘Yan Bindiga Sun Kashe Shi Bayan Sun Karbi Kudin Fansarsa Naira Milyan Shid

Abba yaro ne matashi mai kokarin neman na kansa, masu garkuwa da mutane sun kama shi a hanyar Abuja-Kaduna, suka bukaci sai an biya milyan shida, ‘yan uwansa suka kai kudin ashe sun kashe shi kwanaki biyu, kuma sun amshi kudin, suka ce ‘yan uwansa su je guri kaza su dauki gawarsa.

Irin Abba da yawa an kashe su a hanyar nan babu kuma wani mataki da ake dauka, rayuwar yan kasa ta zama ba abakin komai ba, tun muna jin abunnan a nesa yanzu har ya iso gurinmu an fara kashe kannenmu, wacce irin kasa muke ciki? Wadanne irin shugabanni garemu da ba su damu da mu ba?

Karanta wannan  DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Kama Babban Hafsan Sojin Nigeria Farooq Yahaya

Allah mun kai kukanmu gareka duk mai hannu cikin wannan zaluncin da ake mana, da wadannan azzaluman da ba sa tausayinmu ko cikin watan ibada, Allah ka wulakantasu, Allah ka tona musu asiri albarkacin wannan watan, Wallahi abunnan ya ishe ni. Allah ya isa!!!

Daga Fauziyya D. Suleman

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *