Wasu ‘yan bindiga sun kashe Dayyabu Jafar, wani tsohon kansila yayin da yake aiki a gonarsa da ke Ungwan Fada na Unguwar Gayam da ke karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.
‘Yan bindigar sun kuma kai wa wani mutum mai suna Yusuf Dallatu hari a Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kajuru a wani harin na daban.
Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Gidaje, Samuel Aruwan, wanda ya tabbatar da kisan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce hukumomin tsaro ne suka sanar da abin da ya faru.
Aruwan ya ce sojojin a karkashin inuwar Operation Safe Haven (OPSH) sun bayar da rahoton wani hari da wasu gungun makiyaya suka kaiwa wasu makiyaya da shanunsu a kan hanyar Shanun Mabushi a yankin Zangon Kataf da ke jihar.
A cewarsa, makiyayan, wadanda suke aiki a wa wani Alhaji Usman Abdullahi da ke aiki a Bakin Kogi, karamar hukumar Kauru, suna dauke shanunsu daga Fadan Kaje zuwa Bakin Kogi ta hanyar shanun lokacin da aka far musu.
Ya ce maharan, dauke da adduna da sauran makamai, sojoji sun fatattaki su, wadanda suka amsa kiran gaggawa.
“Dakarun sun samar da kariya ga makiyaya domin kwato shanunsu da suka watse. Dukkan shanu an dawo dasu, banda guda daya wacce daga baya aka gano ta mutu. An kuma raunata saniya daya da adda, ”in ji shi.
Ya ce wani makiyayi, Nasril Musa, wanda ya samu rauni a idonsa na dama, an dauke shi zuwa asibiti inda aka yi masa magani sannan aka sallame shi, ya kara da cewa sojojin sun yi wa makiyayan rakiya zuwa inda suke zuwa a Bakin Kogi, karamar Hukumar Kauru, don hana ci gaba da tashin hankali.
Da yake mayar da martani ga rahotannin, Gwamna Nasir El-Rufai ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda aka kashe ya kuma aika da ta’aziyya ga danginsu.
Dangane da harin da aka kai a karamar hukumar Zangon Kataf, gwamnan ya gode wa sojoji kan yadda suka tunkari mutanen da gaggawa kuma ya bukaci jami’an tsaro da su tabbatar sun yi cikakken bincike game da harin. Ya yi kira da a kwantar da hankula sannan ya bada umarnin a tsaurara tsaro a yankin.