fbpx
Monday, March 1
Shadow

Yan bindiga sun kashe wani dan kasuwa a Jihar Taraba

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa mutane ne, sun kashe wani dan kasuwa a Jalingo, jihar Taraba.

Yan bindigan sun kashe dan kasuwar mai suna Alhaji Abdulrazak Yola a cikin gidansa da tsakar dare, a ranar Juma’a, 12 ga Fabrairu

An bayyana cewa yan bindigan sun yi ta harbi ba kakkautawa kafin su samu damar shiga gidan mamacin, wanda ke Sabon gari a cikin garin Jalingo.

Wani makwabcin mamacin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa manema labarai cewa ’yan bindigar sun harbe shi ne a kirjinsa bayan sun gaza sace shi wanda nan take ya rasu.

Ya ce bayan kashe dan kasuwar, sai ‘yan bindigar suka tsere ta kogin Lamurde suka shiga daji.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *