fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

‘Yan bindiga sun kashe wani malamin jami’ar Poly dake Zamfara bayan sun karbi naira miliyan biyar kudin fansa

‘Yan bindigar da sukayi garkuwa da wani malamin jami’ar Polytechnic, Mr. Sanusi Halilu Kaura dake koyarwa a Abdu Gusau ta jihar Zamfara sun kashe shi.

‘Yan bindigar sun kashe wannan malamin ne bayn sun karbi kudin fansarsa a hannun iyalansa naira miliyan biyar.

Kuma sun kashe shine bayan sunyi garkuwa dashi na tsawon makonni biyar, yayin da aka kai masu kudin fansar nashi a dajin dake tsakanin Kaduna zuwa Zaria ranar talata.

Sai daga bisani suka kira ‘yan uwan nashi suke tabbatar masu da cewa ai ya mutu da dadewa tun lokacin da suke cikin kudin fansar sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.