fbpx
Thursday, March 4
Shadow

Yan bindiga sun kashe wani matashi mai shekaru 27 a Jihar Edo

Wasu ‘yan bindiga da ba a san su ba wadanda ake zargi da kisan gilla sun kashe wani matashi mai shekaru 27 mai suna Adedigba Oluwatosin a yankin Isiohor da ke cikin garin Benin, jihar Edo.

A cewar mai ba da rahoto game da lamarin, marigayin ya shiga harkar buga takardu.

An tabbatar da cewa marigayin yana tattaunawa da ‘yan uwansa yayin da wani wanda ba a san ko waye ba ya kira shi ya nemi ya gan shi kusa da kofar gidansa, inda ya fita don ganawa da mai kiransa.

Yan mintoci kaɗan bayan barinsa, danginsa suka ji karar bindiga kuma suka ruga zuwa waje don ganin abin da ke faruwa, sai suka ga wasu mutane dauke da muggan makamai zaune a cikin mota.

Da ganin su, ‘yan bindigar suka sake bude wuta kan mamacin kuma suna jiran ya mutu kafin su bar wurin, Harbe-harben da suke ya ce ya tilasta wa mutanen Unguwar boyewa.

A lokacin da dangin mamacin suka shiga cikin rajistan kiran wayarsa sun gano cewa wanda ya kira shi na karshe ya kasance macce ce kuma sun yanke hukuncin cewa tabbas an yi amfani da mutumin ne wajen fidda shi daga gida.

Mahaifin mamacin, Mista Asimiyu Adedigba ya shaida wa manema labarai cewa ya kai kara ga Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Edo kan kisan dan nasa, kuma har an fara bincike a kan lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *