fbpx
Thursday, August 11
Shadow

‘Yan Bindiga sun kashe ‘yan Bijilante 30 a jihar Taraba

‘Yan Bindiga sun kashe ‘yan Bijilante akalla 30 yayin da wasu da dama suka bace ba’a san inda suke ba.

 

Lamarin ya farune a karamar hukumar Gasol ta jihar yayin musayar wuta.

 

‘Yan Kungiyar Miyetti Allah ne suka taru dan zuwa su kawar da ‘yan ta’addar amma sai ‘yan ta’addar suka samu labarin zuwansu wanda hakan ne yasa suka musu kwantan bauna suka kashe da dama.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, DSP Usman Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin amma yace ‘yan banga 2 ne kawai aka kashe inda su kuma ‘yan ta’addar an kashe da yawa daga cikinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.