fbpx
Wednesday, February 24
Shadow

‘Yan bindiga sun kashe‘ yan sanda 2 a Delta

Rundunar ‘yan sanda a jihar Delta ta tabbatar da kisan wasu jami’anta biyu da‘ yan bindiga suka yi, a kan hanyar Ugbolu-Illah dake a karamar hukumar Oshimili  da ke jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Mohammed Ali, ya tabbatar da kisan ga manema labarai ranar Talata a Asaba.

Ya ce duk da haka ‘yan sanda sun kashe biyu daga cikin’ yan bindigar, amma anyi rashin sa’a harbe-harben bindiga daga ‘yan sanda yayi sanadin mutuwar wata tsohuwa a yayin artabu da maharan.

Rundunar ta bayyana cewa tana kokarin tattaunawa da Dangin tsohowar domin ganin anyi wani Abu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na daren ranar Asabar a kusa da wani sanannen wurin shakatawa, dake Lake Town Hotel.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *