‘Yan bindiga sun kai hari kwatas din Shola dake Katsina, inda suka kashe hukumar ‘yan vigilanti guda biyu kuma sukayi garkuwa da wasu mutane.
Cikin mutanen da suka yi garkuwa dasu hadda wasu amare sabon aure a cewar wani mazaunin yankin.
Inda ya kara da cewa ‘yan vigilantin sun rasa rayukansu ne yayin da suke kokarin ceto mutanen da ‘yan bindgar sukayi garkuwa dasu.
Yayin da kuma yace wasu ‘yan vigilantin guda biyu sun samu rauni wanda yanzu haka suke asibiti suna jinya.