fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Yan bindiga sun ki sakin ‘yan uwa shida bayan sun karbi kudin fansa naira miliyan biyu a Abuja

Masu garkuwa da mutane shida ‘yan uwa sabon zababben kansila mai wakiltan Yangoji a karamar hukumar Kwali da ke babban birnin tarayya Abuja, Idris Ibrahim sun ki sakin mutanen duk da karbar kudin fansa naira miliyan biyu.

An yi garkuwa da mutanen makonni uku da suka gabata a kauyen Yangoji.

Da farko masu garkuwa da mutanen sun bukaci Naira miliyan 6, amma bayan tattaunawa, sai suka rage kudin zuwa Naira miliyan biyu, inji rahoton Daily Trust.

An kai Naira miliyan 2 ga masu garkuwa da mutanen a ranar Alhamis da ta gabata, 14 ga Afrilu, amma sun ki sakin su tare da neman karin miliyan 3.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.