fbpx
Thursday, June 30
Shadow

‘Yan bindiga sun kona kauye kuma sunyi garkuwa da mutane 30 a jihar Katsina

‘Yan bindiga a ranar sati sun kai hari kauyen Kwari dake karamar Jibiya a jihar Katsina, bayan da jami’ai suka kama masu membobinsu ranar juma’a.

‘Yan bindigar sun kona kauyen Farfanu inda suka jiwa mutane da dama raunuka kuma sukayi garkuwa da yara da mata kusan guda 30.

Amma daga bisani hukumar ‘yan sanda ta koresu. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo ya tabbatar da faruwar lamarin amma sai dai yi wani karin bayani ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Matsalar Tsaro: 'Yan bindiga sunyi garkuwa da shugaban likitoci a jihar Zamfara

Leave a Reply

Your email address will not be published.