fbpx
Friday, August 12
Shadow

‘Yan bindiga sun mamaye dajin kudu masu yammacin Najeriya domin kaiwa Yarabawa hari

Shugaban yarabawan Najeriya, Gani Adams ya bayyana cewa labari yazo masa ‘yan bindiga sun mamaye dajin dake Oyo, Ogun da kuma Osun don kaiwa Yarabawa hari.

A ranar lahadi hadiminsa Kehinde Aderemi ya bayyana hakan inda yace ya kamata gwamnati ta dauki mataki akan lokaci kafin su fara aikata ta’addancin nasu.

Inda yace Najeriya bata taba shiga matsanancin halin matsalar tsaro ba kamar na mulkin shugaba Muhammad Buhari.

Saboda haka shi dai kiran shi ga gwmanatin yanzu shine ya tashi tsaye don magance wannan matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.