Yan Bindigar jihar Naija sun nuna Bidiyon Mutane 21 da suka yi garkuwa dasu inda suke nwman a biyasu kudin fansa Miliyan 500 kamin su sakesu.
Bidiyon ya bayyana inda aka ga ‘yan Bindigar dauke da muggam makamai ciki hadda RPG. Sun rika harbe-harbe a iska.
An ji wata Murya daga cikin mutanen na rokon cewa a taimakesu, Miliyan 500 ake nema. Saidai Tuni Gwamnatin ta Jihar Naija ta bayyana cewa ta kubutar da wasu daga cikin wanda aka yi garkuwa dasu din.
Not only picture, this video they release is more terrifying.
Bandits with grenade launcher? Where are we heading to as nation? pic.twitter.com/dsIOSSu5cc— Ali Musa (@Ali2musa) February 16, 2021