‘Yan Bindiga a jihar Kaduna sun sace wata amarya Tina Moses ana saura kwana daya bikinta a jihar Kaduna.
An shirya daura auren Tina Moses da sahibinta, Elisha Koje a ranar 16 ga watan Afrilu a karamar hukumar Sanga dake jihar Kaduna.
‘Yar uwarta, Esther Attah Asheri ce ta bayyana cewa an saceta ne ranar Juma’a yayin da take kan hanyar zuwa gyaran gashi.
Tace wanda suka sace ta sun tuntubi danginsu amma basu bayyana kudin fansar da za’a basu ba.