fbpx
Monday, March 1
Shadow

Yan Bindiga sun sace babban Malamin Jihar Kaduna

Yan Bindiga sun sace babban Limamin Rigachukun dake jihar Kaduna, Sheikh Muhammad Saminu Adam a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa jihar Naija.

 

Dailytrust ta ruwaito cewa an sace malamin da sauran wasu akan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna ranar Alhamis din data gabata.

 

Sakataren kungiyar Limamai ta jihar Kaduna, Ustaz Yusuf Alrigasiyyu ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Wani mazaunin unguwar ya bayyana cewa an tuntubi iyalan malamin amma ba’a bayyana cewa ko an nemi su biya kudin Fansa ba ko kuwa a’a. Sannan an sanar da sace malamin a madallacin Juma’a.

Yes, we heard about it because he was our member and we are told that they bandits abducted him along Birnin Gwari area,” he said.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *