‘Yan Bindiga a yankin Kunduru sun sace basaraken yankin me shekaru 91 da aka bayyana da sunan Alhaji Ibrahim a jihar Katsina.
Sahara Reporters ta ruwaito cewa Galadiman Kunduru mahaifine ga babban Sakatare a Ofishin gwamna jihar Katsina, Alhaji Kasimu Ibrahim.
An sace basarakenne a daren Ranar Juma’a inda ‘yan Bindigar akan Babura suka shiga garin dauke da manyan makamai.
Hakanan a wani labarin kuma ‘yan Bindigar a karamar hukumar Faskari sun sace mata 12. Matan suna kan hanya daga Funtua zuwa Mai Gora ne karbar wani bashi inda a nanne aka sacesu.
Zuwa yanzu dai ‘yan Bindigar basu tuntubi iyalin wanda suka sace din ba.