fbpx
Monday, March 1
Shadow

Yan bindiga sun sace basaraken gargajiya tare da wasu fasinjojin jirgin ruwa 4 a Jihar Ribas

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne sun sace basaraken gargajiyar (HRM Aarom Ikuru) garin Ikuru da ke cikin Karamar Hukumar Andoni a Jihar Ribas.

Mai magana da yawun fadar, Mista Maurice Ikuru, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a safiyar ranar Litinin, 22 ga Fabrairu, ya ce an sace masarautar ne da misalin karfe 8:30 zuwa 9 na daren Lahadi, 21 ga Fabrairu.

A halin da ake ciki, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Nnamdi Omoni ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ana cigaba da bincike domin samun cikakkun bayanai dange da lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *