‘Yan Bindiga sun sace dalibin jami’ar jihar Kaduna da aka fi sani da KASU.
Lamarin ya farune a yankin Gwantu Kurmi dake karamar hukumar Sanga a jihar, sun kuma sace karin mutum daya.
Hakanan sun jikkata mutum daya wanda aka garzaya dashi Asibiti.
Wanda aka sace din sunansa Joshua Victor kamar yanda Daily post ta ruwaito.