fbpx
Thursday, August 11
Shadow

‘Yan bindiga sun sace mahaifiyar ɗan majalisa a Kano

Wasu ‘yan bindiga sun sace mahaifiyar Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Jihar Kano Isiyaku Ali Danja da tsakar daren Laraba.

Maharan sun shiga gidan Hajiya Zainab da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa da misalin ƙarfe 1:00 na dare ɗauke da makamai, inda suka tilasta wa mutan gidan cewa sai an kai su ɗakinta.

Saminu Danja wanda ɗa ne ga ɗan majalisar, ya faɗa wa BBC cewa ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ɓarayin ba su tuntuɓe su ba.

Honorabul Isiyaku Ali Ɗanja, shi ne tsohon Kakakin Majalisar Kano kuma wakilin Gezawa a majalisar.

Karanta wannan  'Yan ta'addan ISWAP sun kai sabon hari a Maiduguri sun kashe dan samda guda

Yankin arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da fuskantar sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa, sai dai lamarin bai yi ƙamari a Kano ba kamar jihohi maƙotanta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.