fbpx
Saturday, August 20
Shadow

‘Yan Bindiga sun sace mata 20 bayan kisan mazaje a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara a Arewacin Najeriya na cewa mahara sun sace sama da mata 20, biyo bayan jerin hare-hare da suka kai a kauyuka 15 da ke yankin babban birnin jihar, Gusau.

Wasu mazauna kauyukan Geba da Tsakuwa da Gidan Kada da Gidan Kaura da ma karin wasu kauyukan da ke karkashin karamar hukumar ta Gusau, sun shaida wa BBC cewa maharan sun afka musu ne ranar Asabar, inda suka kashe mazaje tare da kona dukiyoyi, suka kuma kwashi mata da yan mata suka wuce da su.

Daya daga cikin mutanen ya fada wa BBC cewa ” ka ga dai Kura sun dauki macce 10 sun tafi dasu. A Bayauri sun dauki tara, sun kuma shiga wani kauye ana kiranshi Gana sun dauki bakwai, daga nan kuma suka ketara Duma suka dauki wasu bakwai kafin wayewar garin Lahadi,” in ji shi.

Bugu da wasu da suke tsallake rijiya da baya a kauyen Kura sun ce an kashe musu mutun bakwai.

A yanzu rahotanni sun ce kauyuka da dama sun fara zama wayam, yayin da mazauna ke gudun hijira zuwa Gusau.

Kamar yadda wani dan gudun hijirar ya shaida wa BBC, yanzu haka sun gudu zuwa anguwar Damba da ke cikin garin Gusau babban birnin jihar ta Zamfara.

“Mata ne da kananan yara ga su nan harda masu ciki ga shi kuma ba abinci. Idan ka ga inda suke kwanciya ga sanyi sai ka ce babu gwamnati,” a cewar wani mazaunin unguwar Damba.

Amma ta ji daga Kwamishinan Yada Labarai na jihar Ibrahim Dosara, wanda ya tabbatar da kai jerin hare-haren, sai dai ya ce jim kadan bayan shigar maharan jami’an tsaro sun kai dauki.

“Akwai sojoji da ke aiki a yankin, kuma sun kai dauki a garin Geba. Lokacin da suka isa mutane uku sun ji rauni kuma sun tarwatsa yan bindigar,” in ji Ibrahim Dosara.

Kwamishinan ya musanta cewa ba a kai wa al’ummar kauyukan sama da 15 dauki ba.

Hare-haren na jihar Zamfara na zuwa a daidai lokacin da hukumomi suka bayyana cewa a ranar Juma’a jami’an tsaro sun kama wasu ‘yan bindiga da aka tarwatsa sansaninsu a wani asibiti suna neman magani.

Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da mahara suka addaba sosai tsawon shekaru, lamarin da a yanzu ya dada kamari a jihohin Sokoto da Katsina da Kaduna masu makwabtaka.

Ko a makonnin da suka wuce ‘yan bindiga sun kona wata motar fasinja dauke da mutum sama da 20 a Sokoto, wani lamari da ya haifar da ce-ce-ku-ce ya kuma fusata wasu ‘yan Najeriya, da ke ganin gwamnatoci sun kyale maharan na cin karensu ba babbaka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.