fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

‘Yan bindiga sun sace mutane 9 da kashe mutum 1 jihar Naija

Rahotanni daga jihar Naija na cewa ‘yan Bindiga sun kama mutane 9 a Kusasu ake yankin Shiroro.

 

‘Yan Bindigar sun je kasuwar garinne akan babura kusan 15 inda suka yi siyayya daga nan kuma suka yi garkuwa da mutane 9. Daga baya sun nemi a biya Miliyan 10 kamin su saki wanda suka yi garkuwa dasu din.

Akwai mutum 1 da yayi yinkurin guduwa amma yan bindigar suka kasheshi shima duk da haka suna neman a biyasu kudin fansa Miliyan 1 akanshi.

 

Lamarin na zuwane bayan da ‘yansanda suka fara kama masu baiwa ‘yan Bimdigar bayanan sirri.

Leave a Reply

Your email address will not be published.