fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Yan Bindiga sun sace mutane da dama a wani mummunan hari da suka kai jihar Sokoto

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun sace kusan mutum 40 a hanyar zuwa Jihar Zamfara daga Sokoto.

Jama’ar da aka sace akasarinsu masu sana’ar sayar da wayoyin sadarwa ne a kasuwar Bebeji Plaza da ke Jihar Zamfara. Rahotanni sun ce sama da mutum 60 ne ƴan bindigar suka tare a hanyar, amma sama da 20 sun samu sun kuɓuta.

Shugaban kasuwar ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin inda ya ce an yi garkuwa da ƴan kasuwar ne a hanyar su ta dawowa daga ɗaurin auren da suka je Sokoto.

Ya bayyana cewa ƴan kasuwar sun tafi ne a cikin mota ƙirar kwasta mai ɗaukar mutum 40 da kuma mota ƙirar bas mai ɗaukar mutum 18.

Mai magana da yawun ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce a halin yanzu jami’ansu na ƴan sanda da sauran jami’an haɗin gwiwa na gudanar da bincike domin gano sauran waɗanda ke hannun ƴan bindigar.

Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da matsalolin ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.