fbpx
Monday, March 1
Shadow

Yan bindiga sun sace Tsohon Jami’in shige da fice da wasu mutum uku a Abuja

An sace wani tsohon Mataimakin Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice ta Kasa, Abdulahi Rakieu da wasu mutum uku a yankin Tungan Maje da ke karamar Hukumar Gwagwalada a Babban Birnin Tarayya.
An ce masu garkuwar sun mamaye gidan wadanda aka yi garkuwar da su sannan suka kwashe su.
Hakan na faruwa ne yayin da rundunar ‘yan sanda ta babban birnin tarayya ta cafke wasu mutane shida da ake zargin masu satar mutane ne a kan hanyar Apo na babban birnin kasar.
Wadanda ake zargin, Frank Ozor, mai shekaru 26, Nweke Uche, 19; Chester Uzor, 25; Chukwu Bethrand, 27; Chukwu Samuel, 25 da Kelechi Ngene, 26, sun shiga hannun jami’an ‘yan sanda da ke sintiri a ranar Asabar, bayan da suka yi awon gaba da mutane uku.
Kakakin rundunar ‘yan sanda, ASP Mariam Yusuf, ta ce an kama wadanda ake zargin a yayin da suke kokarin sauya daya daga cikin wadanda abin ya shafa wuri.
“Karin bincike ya sa aka samu nasarar kubutar da wasu mutum biyu da abin ya rutsa da su wadanda suka gano wadanda ake zargin,” in ji ta a cikin wata sanarwa mai taken, ” Yan sanda sun ceto wadanda lamarin ya rutsa da su, sun kame wadanda ake zargi shida.
Hutudole ya samo, Ta bayyana cewa rundunar ta fara wani shiri na dakile satar mutane don magance matsalar rashin tsaro a babban birnin tarayya.
A cewar ta, ‘yan sanda sun baza jami’an leken asiri a duk fadin Abuja a wani bangare na ayyukan leken asiri a kan masu satar mutane da sauran masu laifi.
Ta ce, “Mun sanya dabarun yaki da aikata laifuffuka na boye da na bayyane don karfafa tsaro a duk fadin Babban Birnin Tarayya.
“Bugu da kari, rundunar tana aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro ‘yan uwa, manyan masu ruwa da tsaki da shugabannin al’umma don kawar da masu aikata laifuka daga babban birnin tarayya.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *