fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Yan bindiga sun sace wani malamin jami’ar Tafawa Balewa, tare da kashe dansa a Zariya, jihar Kaduna

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace Farfesa Aliyu Mohammed na sashen aikin gona na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa satar ta faru ne a daren Lahadi kuma an kashe dan Farfesa, Abdulaziz.
Mista Usman Aliyu, dan farfesan da aka sace, ya shaida wa NAN cewa lamarin ya faru ne ranar Lahadi da misalin karfe 10:30 na dare a Wusasa, Zariya, Jihar Kaduna.
Aliyu ya kuma tabbatar da cewa masu garkuwan sun harbe Malam Abubakar Kabir, wanda kani ne ga marigayin (Abdulaziz Aliyu).
Ya ce bai jima da komawa gidan ba da misalin karfe 10.30 na daren Lahadi, sai ya ji karar harbe-harbe ba zato ba tsammani sai ya buya ta wani wuri a cikin gidan.
A cewarsa, lokacin da harbe-harben suka tsaya, ya kira wani kaninsa wanda ya sanar da shi cewa su (‘yan bindigar) sun kashe dan uwansu kuma sun yi awon gaba da mahaifinsu.
Ya kara da cewa tuni aka yi jana’izar mamacin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, yayin da wanda aka harba ke karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.
Alhaji Ahmad Amfani, Hakimin Kuregu, Wusasa, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa kokarin da aka yi na jin ta bakin hukumomin tsaro bai yi nasara ba domin babu wanda ya amsa kiran gaggawan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *